<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>520</hymn_number>
<title>Tsakanina da Mai Cetona LW520</title>
<lyrics>[V1]
 1) Tsakanina da Mai Cetona
 Ba zan bi ruɗin duniya ba,
 Na bar nishatsin wannan duniya,
 Sai dai Yesu ne, ni ke sonsa.

[V2]
 KORUS
 Tsakanina da shi, babu kome
 Da zai hana in ga fuskarsa.
 Alherinsa ba zai hannu ba
 In na tabbatadda zuciyata.

[V3]
 2) Me zai raba ni da Mai Ceto,
 Ko raɗaɗi da ruɗin Shaiɗan?
 Duk waɗannan ba zai raba mu ba,
 Shi ne kaɗai zan manne masa.
 Korus

[V4]
 3) Ba fahariya ko alfarma,
 Ko ni kaina ko abokai,
 Ko da shi ke zan sha tsanani,
 Duka da haka Shi ni ke so.
 Korus

[V5]
 4)Ko jaraba ta taso mani
 Ko duniya tana ƙi ni.
 Addu'a za ta ba ni nasara.
 Ba abin da zai hana.
 Korus</lyrics>
</song>